Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar dattijan Najeriya sun dakatar da mika makuridn Bakassi ga kamaru


Majalisar dattijan Najeriya sun bukaci shugaba Umar ‘Yar’adua ya dakatar da mika makuridn Bakassi ga kamaru. A wani kuduri da senatoji 21 suka gbatar,jiya Alhamis Majlisar tace tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a kashin kansa ya sanya hanu kan takardar mika makurdin ga kamaru,wadda yin haka ya sabawa tsarin Mulkin kasa.

Senatocin sunbukaci a basu damar suyi muhawara kuma su amince da yarjejeniyar mika yankin. Haka kuma kudurin yayi la’akari da zaman dar dar a makurdin a baya bayan nan.Idan zaa iya tunawa an kashe sojojin kamaru 21 ranar 12 ga watan nan a can.

Hukumomin Najeriya sun aza laifin kai harin kan tsageru dake kudancin kasar, sannan su kuma tsagerun suka aibanta sojojin najeriya. Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya amince da mika makurdin mai arzikin Mai ga kamaru cikin watan Yunin bara,bisa hukuncin da kotun kasa da kasa ta yanke.Akwai karin bayani bayan labarai.

XS
SM
MD
LG