Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rage Cin Gishiri Zai Ceci Ran Miliyoyin Mutane Daga Cutar Zuciya Da Ta Sankara A Duniya


Wasu masana kimiyya daga kasashen duniya dabam-dabam sun wallafa sakamakon wani bincike wanda ya nuna cewa za a iya ceton rayukan miliyoyin mutanen dake mutuwa daga cutar zuciya da sankara cikin shekaru goma dake tafe idan har mutane zasu rage yawan gishirin da suke ci.

Masana kimiyyar, wadanda aka wallafa binciken nasu jiya talata cikin mujallar aikin likita mai suna Lancet, sun nazarci yadda za a iya cimma gurin da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta kafa a 2005, na rage yawan mutane masu mutuwa daga munanan cututtuka da kashi biyu cikin 100 kowace shekara na tsawon shekaru goma.

Masu bincike sun nazarci irin amfanin rage yawan gishirin da mutane ke ci da kashi 15 cikin 100 a kasashe 23 inda aka fi fama da munanan cututtuka a duniya, ciki har da Amurka da Nijeriya, da Rasha da Indiya da Vietnam da Ethiopia da Burma.

Masana kimiyyar suka ce idan mutane a wadannan kasashen zasu dauki wasu ’yan kananan matakai kamar gujewa abinci mai gishiri, da rage yawan gishirin da suke sanyawa cikin miya, to ana iya ceton rayukan mutane miliyan 8 da dubu dari biyar nan da shekara ta 2015.

XS
SM
MD
LG