Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Zai Tura Manyan Mukarrabai Biyu Don Su Tattauna Da Shugaba Omar al-Bashir Na Sudan.


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Ban Ki-moon, ya ce zai tura wasu manyan mukarrabansa su biyu domin lallashin shugaban Sudan da ya yarda da sojojin da ba na Afirka ba a cikin rundunar kiyaye zaman lafiya a Darfur.

Mr. Ban ya ce yau alhamis manyan jami’an su biyu zasu tafi kasar Portugal domin ganawa da shugaba Omar al-Bashir. Shugaba Bashir yana kasar Portugal ne domin taron kolin Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka da Kungiyar Tarayyar Turai da za a yi cikin wannan makon.

Shugaba Bashir ya nuna adawa da shirin sanya sojojin kasashen Nepal da Thailand da kasashen yankin Scandinavia a cikin rundunar kiyaye zaman lafiya a Darfur. Akasarin sojojin wannan runduna mai sojoji dubu 26 sun fito ne daga kasashen Afirka.

A wani labarin kuma, Kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya ta roki Kwamitin Sulhun MDD da ya matsa lamba kan Sudan da ta mika wasu mutane biyu da ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki a Darfur. Mai gabatar da kararraki a gaban kotun, Luis Moreno Ocampo, ya ce gwamnatin Sudan tana yin ko oho da kotun ta hanyar bayar da kariya ga mutanen biyu da aka tuhuma.

XS
SM
MD
LG