Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi Kimanin Miliyan Biyu Suke Tsayuwar Arafat


A yau talata Musulmi kusan miliyan biyu suke tsayuwar Arafat, a rana ta biyu da fara ayyukan ibada na aikin Hajjin bana.

Jiya litinin, mahajjata a cikin farin harami (wanda ke nuna alamar tsarki) sun bar birni mai tsarki ga Musulmi na Makka, suka isa zuwa ga dubban tantunan da aka kafa a kwazazzabon Mina, inda suka kwana.

Kamfanin dillancin labarai na Sa'udiyya, ya ce duk da yawan motoci da masu tafiya a kafa, an gudanar da ayyukan ibada na ranar farko ba tare da wata tangarda ba. Wani mahajjaci daga Jihar California a yammacin Amurka, Hisham el-Khatib, ya ce abu ne mai girgiza zuciya da ban al'ajabi mutum ya kasance cikin irin wannan taro na Musulmi daga kowace kusurwa ta duniya.

Irin wannan taron ibada na mutane bila'adadin yana haifar da kalubale na kayan aiki da kuma kula da lafiyar jama'a ga hukumomin Sa'udiyya, wadanda suka ce su na daukar matakan kare bazuwar masassarar tsuntsaye. Kwanakin baya cutar ta murar tsuntsaye ta kashe tsuntsaye a wata gona mai tazarar kilomita tamanin a kudu da Riyadh, babban birnin kasar.

Shugaba Mahmoud Ahmadinejad na Iran yana halartar aikin Hajjin na bana, kuma a jiya talata ya ziyarci Masjidil Nabiy a Madina. Shi ne shugaban Iran na farko da ya je shi aikin Hajjin.

Aikin Hajji yana daya daga cikin shika-shikai biyar na Musulunci, kuma farilla ne ga kowane Musulmi, mai karfi da hali da kuma lafiya, yayi shi sau daya a rayuwarsa.

XS
SM
MD
LG