Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar NPP Mai Mulkin Ghana Ta Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasarta


Jam’iyyar New Patriotic Party, NPP, mai mulkin kasar Ghana, ta zabi tsohon Ministan Harkokin Wajen Kasar, kuma dan tsohon Shugaban Kasa, Nana Akufo-Addo, a matsayin dan takararta na Shugaban Kasa, a babban zaben kasar da za a gudanar a shekara mai shigowa.

Shugaban na yanzu, John Kufuor, zai kammala wa’adi na biyu, kuma ba shi da ikon sake tsayawa takara domin yin wani wa’adin.

A jiya Lahadi aka zabi Akufo-Addo mai shekaru 63 da haihuwa, a matsayin shugaban jam’iyyar, kuma dan takararta na shugabancin kasa, bayan ya sami kashi 48 bisa dari na kuri’un da kimanin wakilai dubu biyu suka kada.

Wanda ke biye da shi, daga cikin ‘yan takara 17, Alan Kyeremantang, wanda kuma ya sami kashi 32 bisa dari na kuri’u, ya rungumi kaddara, ya kuma nuna goyon bayansa ga Akufo Addo, al’amarin da yasa aka kaucewa komawa zagaye na biyu na zaben.

A zaben na watan Disambar 2008, dan takarar jam'iyyar ta NPP zai kara da tsohon mataimakin shugaban kasar Ghana, John Atta Mills, na babbar jam'iyyar hamayya ta National Democratic Congress, ko NDC.

Nana Akufo-Addo lauya ne da yayi karatu a kasar Britaniya, kuma daya daga cikin mutanen da suka fara kafa jam'iyyar NPP a shekarar 1992. Shi ne babban dan tsohon shugaban kasar Ghana, Edward Akufo-Addo, wanda ya shugabanci kasar a cikin shekarun 1970.

XS
SM
MD
LG