Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Tsohuwar Firayim Ministar Pakistan, Benazir Bhutto


A ranar jumma'a aka yi jana'izar tsohuwar firayim ministar Pakistan, Benazir Bhutto, wadda aka yi wa kisan gilla ranar alhamis ta makon jiya. Dubban magoya bayanta ne suka halarci jana'izar marigayiyar, wadda aka binne dab da kabarin mahaifinta, Zulfikar Ali Bhutto, a garinsu na haihuwa dake lardin Sindh a kudancin kasar.

Mijinta da sauran dangi ma sun halarci halarci jana'izar.

Kashe Malama Bhutto ya haddasa tashe-tashen hankula masu muni a biranen Pakistan da dama, ciki har da Rawalpindi, inda aka kashe ta. An kashe mutane akalla tara a tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan kisan gillar.

An sanya illahirin sojojin Pakistan cikin shirin ko-ta-kwana a yayin da 'yan zanga-zangar dake fusace suka yi ta cunna wuta a motoci tare da farfasa kantuna a biranen Karachi da Lahore da wasu wuraren.

An kashe Malama Bhutto, daya daga cikin manyan 'yan adawar Pakistan, a daidai lokacin da take barin wani wurin gangamin yakin neman zaben majalisar dokokin da aka shirya gudanarwa ranar 8 ga watan Janairu.

'Yan sanda suka ce dan harin kunar-bakin-wake ya harbi Malama Bhutto, sannan ya tarwatsa kansa daga bisani ya kashe wasu mutanen su akalla ashirin.

Gidan telebijin na CNN ya fada jiya alhamis cewa kakakin Malama Bhutto a Amurka, Mark Siegel, ya ce ya samu wata wasika ta Email daga Bhutto a watan Oktoba. A cikin wasikar, ta ce duk wani abinda ya same ta, to a tuhumi shugaban Pakistan Pervez Musharraf.

Wannan sakon da aka rubuta watanni biyu da suka shige, ya ambaci Malama Bhutto tana fadin cewa 'yan barandar Musharraf su na yi mata barazana. Har ila yau ta zargi shugaban da laifin hana ta shiga motar kanta, ko kuma yin amfani da mota mai duhun gilashi.

Malama Bhutto tana cikin mota mai sulke a lokacin da aka kai mata hari, amma kuma abin kaddara, ta kunno da kanta da kuma kafadarta waje ta cikin gilashin saman motar tana daga hannu ga magoya baya sai dan harin ya harbe ta.

An garzaya da ita zuwa wani asibiti, amma likitoci sun kasa farfado da ita. Ta rasu tana da shekaru 54 da haihuwa.

Shugaba Musharraf ya dora laifin mutuwarta a kan 'yan ta'adda, ya kuma ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku. Shugaban ya roki al'ummar Pakistan da su kwantar da hankulansu.

XS
SM
MD
LG