Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Jami'in Diflomasiyyar Amurka A Sudan


An kashe wani jami’in diflomasiyya na Amurka tare da direbansa a wani harin da aka kai musu kafin fitowar rana jiya talata a Kahrtoum, babban birnin Sudan.

Hukumar Tallafawa Kasashe Masu Tasowa ta Amurka ta bayyana cewa jami’in da aka kashe shi ne John Granville mai shekaru 33 da haihuwa. Jami’ai sun ce ya mutu a asibiti sa’o’i da dama a bayan da aka harbe shi sau biyar a hannu da kafada da kuma ciki.

Direbansa, Abdulrahman Abbas dan kasar Sudan mai shekaru 40 da haihuwa ya mutu nan take.

Gwamnatin Sudan ta ce ’yan bindiga sun bude wuta a kan motar jami’in diflomasiyyar na Amurka da misalin karfe 4 na asuba a kan titunan birnin Khartoum. Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta bayyana lamarin a zaman farmaki na kaddara, ba wai wanda aka kitsa bisa dalilan siyasa ba.

Kafofin labaran Sudan sun ambaci wani jami’in gwamnati yana fadin cewa babu wata shaidar cewa harin na ta’addanci ne.

XS
SM
MD
LG