Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata nakiyar da aka binne a kasa ta halaka darektan gidan rediyon R et M, a Niamey


Jami’an gwamnatin kasar jamahuriyar Nijer sun ce fashewar wata nakiyar da aka binne a kasa ta halaka darektan gidan rediyon R et M, mai zaman kan shi a Niamey babban birnin kasar.

Wani dan jarida mai suna Khader Idy ya ce Abdou Mahaman Jeannot na kan hanyar zuwa gida jiya da daddare lokacin da motar shi ta ci karo da nakiyar. Wata mata da ke cikin motar tare da shi, ta ji ciwo kada, amma daga bisani an sallame ta daga babban asibiti.

Yau laraba jami’an tsaron kasar jamahuriyar Nijer sun gano, wata nakiya ta biyu, wadda ba ta fashe ba a wajejen. Su na ci gaba da karake yankin su gani, ko da sauran nakiyoyi a binne. Kakakin gwamnatin kasar jamahuriyar Nijer Ben Omar Mohammed ya ce, dole ne kaukacin al’ummar kasar ta Nijer ta kara maida hankali.

Ya ce har yanzu ba’a san wanda ya dasa nakiyoyin a birnin Niamey ba, amma ya ce, ya na zargin kungiyar ’yan tawayen MNJ. Kakakin kungiyar ’yan tawayen, Aoutchiki Mohammed Kriska, ya musanta cewa su na da hannu a cikin fashewar nakiyar, ya ce ’yan tawayen ba su taka neman kai hari kan fararen hula ba.

XS
SM
MD
LG