Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata kungiyar Amurka tan kira ga Gwamnatin Turkiyya ta matsawa shugaban Sudan Umar al-Bashir ya kawo karshen ta’asar da ake tabkwa a yankin Darfur


Wata kungiyar kare hakkin bil’adama dake da zama anan Amurka tan kira ga Gwamnatin Turkiyya ta matsawa shugaban Sudan Umar al-Bashir, wadda yake fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a Ankara a yau litinin,ya kawo karshen ta’asar da ake tabkwa a yankin Darfur da yaki ya dai dai ta.

A sanarwar da ta bayar a jiya Lahadi,kungiyar Human Rights watch, tace tayi mamakin Turkiyya ta gayyaci al-Bashir.Kungiyar tana aibanta shuagaban na Sudan da “mummunar keta hakkin bil’adama bila adadin” a Darfur. Kungiyar tace Turkiyya da sake jaddada matsayinta wajen mutunta hakkin bil’adama ta kiran Mallam al-Bashir ya kawo karshen danyar da ake tafkawa.

Human Rights watch ta kuma yi Allah wadai da shawarar Gwamnatin Sudan, na baiwa shugaban kungiyar mayakan sakai na Janjawaeed, mukamin Gwamnati. Hukumomi sunce an nada Musa Hilal, shugaban Janjaweed,mai bada shawara ga Ma’aikatar kasa ta Sudan.

XS
SM
MD
LG