Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asusun Tallafawa Yara Na Majalisar Dinkin Duniya Yace Rayuwar Yara Tana Kyautatuwa A Fadin Duniya


Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya ce rayuwar yara tana kyautatuwa a fadin duniya, amma har yanzu akwai sauran aiki, musamman a kasashen bakar fata na Afirka.

A cikin rahotonsa na shekara-shekara kan halin da yara suke ciki a fadin duniya, asusun na UNICEF ya fada jiya talata cewa a karon farko tun 2006, yawan yaran da suke mutuwa kafin su cika shekaru 5 da haihuwa ya ragu zuwa kasa da miliyan 10 a duniya.

Amma babbar darektar asusun, Ann Veneman, ta ce yawan yaran dake mutuwa ya wuce kima. Ta fadawa Muryar Amurka cewa kimanin rabin yaran dake mutuwar duk a nahiyar Afirka suke. Ta kara da cewa yaron da aka haifa a kasashen bakar fata na Afirka yana fuskantar kasada daya cikin 7 ta mutuwa kafin ya cika shekaru biyar da haihuwa.

Rahoton asusun ya ce yara suna mutuwa daga cututtuka kamar gudawa, maleriya da rashin abinci mai gina jiki. Ya ce ana iya rigakafin akasarin wadannan mace-mace ta hanyoyi masu sauki kamar yin allurar rigakafi, da amfani da gidan sauro da aka jika da magani da kuma shan magungunan kara lafiyar jiki na Vitamins.

XS
SM
MD
LG