Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau  shugaba Bush zai gabatar da jawabin da halin da kasa ke ciki na shekara shekara a gaban Majalisar dokokin Amurka.


A yau litinin ce shugaba Bush zashi gaban Majalisar dokokin Amurka domin gabatar da jawabin kasafin kudin da halin dai Amurka na ciki na shekara shekara. Da shike wannan itace shekarar karshe a Mulkin Bush,mukarraban sa a Fadar white House sunce ba zai bata lokaci wajen waigawa ya dubi lamuran da suka wuce ba.

Maimakon haka rahoton sa ga Majalisa da kuma Amurkawa zai fi maida hankali kan hangen gaba da kuma lissafa muhimman abubuwa da zai fi maida hankali kansu a shekararsa ta karshe a kan mulki.

Ana sa ran Mr. Bush zai kirayi Majalisar Dokoki ta zartas da kudurin kasafin kudi na wucin gadi domin zaburad da tattalin arzikin Amurka ta wajen samara da sauki ga kamfanoni, ‘yan kasuwa da kuma mutane, domin hana lamarin kara tabarbarewa.

Gameda tsaro kuma,ana jin shugaba Bush zai bukaci Majalisar ta sake sabunta dokar nan da ta jawo cacar baki wacce ta baiwa Gwamnati izinin sauraron hirarraki tsakanin Amurkawa ko mazauna kasar da mutane daga kasashen ketare da ake tuhumar da alaka da ta’addanci.

XS
SM
MD
LG