Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama, dan Majalisar ya sake samun nasara


Dan Majalisar Dattijai Barack Obama, ya sake samun nasara a jerin nasarori da ya samu a baya bayan nan,da lashe ‘yar tinke da akayi jiya lahadi a Jihar Maine, dake arewa maso gabashin kasar. Obama ya kada abokiyar takarar sa da samun kashi 59 sannan Hillary Clinton kuma ta sami kashi 40.

Haka kuma Obama ya sami nasara a zabubbuka da ‘yar tinke da akayi ranar Asabar a jihohin Lousiana,Nebraska,Jihar Washington,da ma yankin tsibirin Virgin dake karkashin ikon Amurka.Hudu daga cikin nasarorin nasa ya samu da kamar kashi 20 cikin dari na kuri’u da aka kada ko ma fiye da haka.

‘Yan Malisar Dattijan biyun suna takara a zaben sharen fagen da ‘yar tinke a duk fadin Amurka,suna yakin neman zabe tsaida su takarar shugabancin Amurka a zaben kasa da za;ayi cikin watan Nuwamban bana. Jiya lahadi Ms.Clinton ta sake shugabar yakin neman zaben ta.

Jami’an Kamfen din Malama Hillary sunce Maggie William wacce da jumawa ta hanun damar Hillary ce zata karbi shugabancin yakin neman zaben a wani lokaci cikin wannan mako daga shugabar mai barin gado Patty Solis Doyle,wacce ita ma da jumawa tana tare da Hillary Clinton.

XS
SM
MD
LG