Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sashen Hausa Na Muryar Amurka Zai Gudanar Da Tarurrukan Kiwon Lafiya A Birane Hudu A Nijeriya


Sashen Hausa na Muryar Amurka, ya kammala shirye-shiryen gudanar da tarurruka kan yaki da cututtukan yara kanana da na mata a wasu birane guda hudu a yankunan arewa maso yammaci da kuma arewa maso gabashin Nijeriya.

A cikin wata sanarwar da ya bayar a Washington, shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Sunday Dare, ya ce makasudin wadannan tarurruka shi ne janyo hankali tare da kara wayar da kan jama'a game da matakan da zasu iya dauka na kare yara da mata daga cututtuka masu saukin rigakafi ko saukin warkarwa.

Shugaban na Sashen Hausa ya ce su ma gwamnatoci da hukumomin lafiya masu zaman kansu zasu iya kara fahimtar irin matsalolin da jama'a suke fuskanta a fannin kiwon lafiya.

Za a gudanar da taron farko ranar Litinin, 3 ga watan Maris a Gusau, hedkwatar Jihar Zamfara a dakin taron nan da ake kira J.B. Secretariat, daga karfe 11 na rana.

Za a yi taro na biyu ranar Alhamis, 6 ga watan Maris a Birnin Kebbi, hedkwatar Jihar Kebbi a dakin taro na Presidential Lodge, daga karfe 11 na safe.

Taro na uku, za a gudanar da shi ranar Asabar, 8 ga watan Maris a Makarantar Nazarin Qur'ani ta Sultan Maccido, daga karfe 10 na safe.

Taro na hudu kuwa, za a gudanar da shi ranar Alhamis, 13 ga watan Maris a Maiduguri, a dakin taro na State Hotel daga karfe 11 na safe.

Manyan baki a wadannan tarurruka sun hada da gwamnoni, da sarakuna, da kwararru a fannin kiwon lafiya wadanda zasu gabatar da bayanai tare da amsa tambayoyin jama'a a zauren taro.

Edita a Sashen Hausa na Muryar Amurka, Ibrahim Alfa Ahmed, shi ne zai gabatar da tarurrukan da masu jawabai.

Haka kuma, za a gudanar da gasar kiwon lafiya a dukkan wuraren tarurrukan, inda za a rarraba akwatunan rediyo masu nagarta samfurin Eton E100 da Grundig G1000-A. Akwai kuma wasu kyaututtukan kamar riguna da huluna, da alkaluma da baji da kasidu na kiwon lafiya da za a rarraba a zauren taro.

Ana gayyatar dukkan masu sauraro a wadannan yankuna da su halarci wuraren tarurrukan.

XS
SM
MD
LG