Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun kolin Amurka tana sauraron gagarumar shari’a game da hakkin Amurkawa na mallakar bindiga


Kotun kolin Amurka tana sauraron gagarumar shari’a game da hakkin Amurkawa na mallakar bindiga.

A yau talata kotun tana sauraron muhawara kan ko ta amince da dokar da gundumar Kolombiya ta kafa shekaru 32 da suka wuce na haramtawa mazauna cikin yankin mallakar bindiga.

Haka kuma kotun tana sauraro haramcin dsa gundumar ta kafa gameda adana kananan makamai da bindgogin Rifle. Daga karshe dai ana sa ran hukuncinda zata yanke yana da muhimmanci domin zai fayyace abinda tsarin Mulkin Amurka ke nufi da kalamansa dake cewa “Hakkin Mallakar Makamai,a cikin kwaskwarima na biyu da akayiwa tsarin Mulkin.

Kotun bata yanke hukunci kan batun ikon mallkar makamai ba tun alif dari tara da talatin da tara.

XS
SM
MD
LG