Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar David Petraeus Da Jakada Ryan Crocker Sun Bayar Da Shaida Game Da Yakin Iraqi


Babban kwamandan sojojin Amurka a Iraqi ya bayyana dari-darin ajiye lokaci na janyewa daga Iraqi, yana mai fada wa majalisar dokoki cewa ci gaban da aka samu bai zauna sosai yadda ya kamata ba.

Janar David Petraeus ya fadawa Kwamitin Kula da Ayyukan Soja na Majalisar Dattijai a yau talata cewa ya kamata Amurka ta janye karin sojoji dubu 30 da ta tura Iraqi a shekarar da ta shige nan da watan Yuli. Amma yace daga nan, ya kamata kwamandojin dake can su nazarci halin tsaro na wasu kwanaki 45 kafin a yanke shawarar ko za a iya maido da karin sojoji gida.

Janar Petraeus da jakadan Amurka a Iraqi, Ryan Crocker suna bayar da shaida a gaban kwamitocin majalisar dokoki yau talata da kuma gobe laraba. Crocker, a nasa bangaren, yayi gargadin cewa sauya alkiblar manufofin Amurka na yanzu a Iraqi na iya kawo faduwa.

XS
SM
MD
LG