Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somaliyawa Shida Sun Isa Faransa


Jami’ai sun ce wasu Somaliyawa da ake zargin cewa ’yan fashi cikin teku ne su 6, wadanda kuma ake zargi da yin fashin wani jirgin ruwan shakatawa na Faransa a kusa da gabar Somaliya sun isa kasar Faransa inda za a gurfanar da su gaban kotu.

A yau laraba aka kai mutanen shida Faransa a cikin wani jirgin saman soja, kuma nan take aka damka su hannun hukumomin kurkuku.

Sojojin Faransa sun damke mutanen ranar jumma’a a cikin Somaliya a bayan da aka sako ma’aikatan jirgin ruwan su 30 da aka yi garkuwa da su. 22 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su Faransawa ne.

Jami’an Faransa sun jira sai da suka samu izni daga hukumomin Somaliya kafin kai mutanen Faransa don yi musu shari’a.

XS
SM
MD
LG