Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fernando Lugo ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi jiya lahadi a kasar Paraguay


Dan takarar hamayya Fernando Lugo ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi jiya lahadi a kasar Paraguay, abinda ya kawo karshen mulkin shekaru 61 da jam’iyyar Colorado ta yi.

Lugo ya doke ’yar takarar jam’iyya mai mulki Blanca Ovelar, wadda jiya da daddare ta mika wuya ta ce ta sha kaye, ta kawo karshen yunkurinta na zamowa macen farko da zata zamo shugabar kasar.

Mr. Lugo yayi alkawarin tallafawa talakawan kasar. Shi dai Lugo tsohon babban fada na ’yan darikar Roman Katolika ne mai mukamin Bishop, kuma shine ya zamo dan takara na gamayyar jam’iyyun hamayya da suka hada da babbar jam’iyyar hamayyar kasar, da kungiyoyin kwadago, da kungiyoyin manoma da kuma Indiyawan daji. A can baya, mutane suna kiran Lugo da sunan Limamin Talakawa.

XS
SM
MD
LG