Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar kungiyar ’yan tsageran a kudancin Nigeria  ta sake fasa wani bututu mallakar kamfanin Shell


Babbar kungiyar ’yan tsageran da ta kai manyan hare hare na baya bayan nan a kudancin Nigeria mai arzikin man fetir tace ta sake fasa wani bututu mallakar kamfanin Shell na Birtaniya.

A cikin wata sanarwa da ta aika ta hanyar e-mail, kungiyar Movement for the Emancipation of Niger Delta-MEND, tace ’yan bindiga dadinta sun kai hari kan bututun ne jiya da dare. Wannan ne bututun kamfanin Shell na hudu da kungiyar ta kaiwa hari cikin wannan watan. Jami’an kamfanin Shell basu tabbtar da wannan batun ba.

Yan bindiga dadi da kungiyoyin ’yan tsagera sun fara kai hare hare kan kamfanonin mai a Delta ne cikin shekara ta dubu biyu da biyar suna neman karin kason kudin shiga da ake samu daga albarkatun man fetir a yankin da talauci ya yi kanta.

XS
SM
MD
LG