Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A kasar Burma, mutane dubu hudu  suka halaka daga mummunar guguwar teku 


Jami’an kasar Burma sun kara adadin mutane da suka halaka sakamakon mummunar guguwar teku da aka lakabawa sunan Nargis daga 350 zuwa dubu hudu. Gidan talabijin na kasar a yau litinin ya sanar da karin salwantar yayinda aka sami bayanai daga sassan kasar masu nesa inda guguwar ta yi mummunar barna ranar Asabar.

Haka kuma jami’an suka ce kusan mutane dubu uku sun bata. Farashin abinci da mai sunyitashin gworon zabbi tun Asabar din. Kungiyoyi tallafi suna gaggawar kai kayan agaji ga dubun dubatan mutane da suka rasa muhallan su. A jiya lahadi Gwamnatin Mulkin Sojan kasar ta ayyana Rangoon da wasu jihohi biyar dake tsakiya da kudancin kasar matsayin yankuna da bala’I ya afkawa.

Mazauna yankunan suna kukan tafiyar hawainiya daga Gwamnati sojan kasar wajen tinkarara wannan lamari.MDD tace a shirye take ta taimaka,amma har zuwa yau Gwamnati bata bukaci taimako daga hukumomin kasa da kasa ba.

Ma’aikatan agaji na MDD sunce ba za su shiga Burma ba ta reda izini ba. Duk da wannan barna da guguwar tayi Gwamnatin Mulkin Sojan kasar tace za a ci gaba shirin kuri’ar raba gardama ranar Asabar.

XS
SM
MD
LG