Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako 'Yan Kasar Sin Da Aka Sace Aka Yi Garkuwa Da Su A Kudancin Nijeriya


Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce an sako wasu ma'aikatan kasar masu aikin kwangila su uku da aka sace cikin wannan makon a kudancin Nijeriya. Wata gajeruwar sanarwar da aka bayar asabar ta ce an sako ma'aikatan Kamfanin GineGine na Sin a ranar jumma'a.

Sanarwar ba ta bayar da karin bayanin yadda aka sako mutanen ko kuma jami'an kasar Sin sun biya kudin fansa ba.

A ranar talata wasu 'yan bindiga suka sace ma'aikatan a kusa da gidan kamfaninsu a Calabar, babban birnin Jihar Cross River.

Kungiyoyin 'yan tsagera da na 'yan daba su na yawaita sace ma'aikata 'yan kasashen waje a yankin Niger-Delta mai arzikin man fetur, akasari don neman kudin fansa a hannun na kusa da su ko kamfanoninsu. Akasari a kan sako mutanen ba tare da ko kwarzane ba.

XS
SM
MD
LG