Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Morgan Tsvangirai Ya Fasa Komawa Zimbabwe Asabar Din Nan


Shugaban jam’iyyar hamayya ta kasar Zimbabwe ba zai koma gida kamar yadda ya shirya a yau asabar ba, a saboda dalilai na tsaro.

Wani kakakin jam’iyyar MDC ya ce sun samu bayani daga wata majiya mai tushe dangane da makarkashiyar da aka kitsa ta kashe Morgan Tsvangirai. Mr. Tsvangirai ya bar kasar Zimbabwe tun zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki na ranar 29 ga watan Maris.

Sakamakon da hukuma ta bayar ya nuna cewa ya doke shugaba Robert Mugabe a zaben, amma bai samu fiye da rabin kuri’un da aka jefa, wanda ake bukata, don lashe zaben kai tsaye ba tare da yin zagaye na biyu ba.

Tun fari, an sa ran shugaban na jam’iyyar MDC zai koma daga kasashen Turai don fara yakin neman zaben zagaye na biyu na fitar da gwani da za a yi tsakaninsa da Mr. Mugabe ranar 27 ga watan Yuni. Jam’iyyar ta shirya wani gagarumin gangami gobe lahadi.

XS
SM
MD
LG