Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Hamayya Ta Kasar Zimbabwe Ta Yi Alkawarin 'Binne' Robert Mugabe


Babbar jam'iyyar hamayya ta kasar Zimbabwe ta yi alkawarin "binne" shugaba Robert Mugabe a zaben fitar da gwani da za a gudanar ranar 27 ga watan Yuni.

Jam'iyyar "Movement for Democratic Change", ko MDC a takaice, ta yi wannan alkawarin a lokacin da ta ke kaddamar da yakin neman zabe a wajen wani gangamin da ta gudanar a birnin Bulawayo.

A lokacin da yake jawabi ga magoya baya su kimanin dubu goma, mataimakin shugaban jam'iyyar MDC, Thokozani Khupe, ya ce jam'iyyar zata lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da ratar da ta fi wadda ta ba Mugabe a zaben farko.

An gudanar da wannan gangami ba tare da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta MDC, Morgan Tsvangirai, ba a saboda ya jinkirta komawarsa kasar a dalilin makarkashiyar da aka yi zargin ana kullawa ta kashe shi. Gwamnatin Zimbabwe ta ce wannan zargin ba ya da tushe, kuma Mr. Tsvangirai yana neman samun wata moriyar siyasa ce kawai cikin sauki daga irin wannan zargin.

A zaben fitar da gwanin da za a gudanar, Mr. Tsvangirai yana fatar doke shugaba Mugabe wanda ya shafe shekaru 28 yana mulkin kasar Zimbabwe.

XS
SM
MD
LG