Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Kakakin Shugaba George Bush Ya Rubuta Sabon Littafin Dake Zargin Shugaban Da Yaudarar Duniya Kan Batun Iraqi


Wani tsohon kakakin shugaba George Bush na Amurka, Scott McClellan, ya fada cikin wani sabon littafi cewa shugaban ya jagoranci wani gangamin farfaganda, da nufin "yaudarar majiyoyin dake tasiri ga ra'ayoyin jama'a" don samun goyon bayan Amurkawa ga yakin Iraqi.

A wasu sassa na wannan littafi mai shafi 341 da za a walafa a mako mai zuwa, McClellan, wanda ya rike mukamin sakataren yada labarai na fadar White House an shekaru uku daga shekarar 2003, ya rubuta cewa Mr. Bush bai fito ya fadi gaskiya ba game da batun Iraqi.

A cikin wata sanarwar da ta bayar yau laraba, mai magana da yawun fadar White House, Dana Perino, ta bayyana tsohon abokin aikin nata a zaman wanda ransa ke bace da rashin samun wani abu, ta kuma ce ma'aikatan ofishin sun kasa fahimtar dalilan da zasu sa McClellan yin wannan zargi. Perino ta ce ba a sa ran Mr. Bush zai ce uffan game da littafin.

Har ila yau kuma, McClellan ya soki gwamnatin Mr. Bush a saboda yadda ta takali irin mummunar barnar da mahaukaciyar guguwa ta Katrina ta yi a shekarar 2005, yana mai fadin cewa fadar White House ta shafe makon farko da faruwar bala'in tana neman kin yarda da abinda ya faru ko musanta shi.

XS
SM
MD
LG