Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talata Za A Gudanar Da Zabubbuka Biyu Na Karshe Na Fitar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar Democrat


’Yan majalisar dattijai Hillary Clinton da Barack Obama, dukkansu ’yan jam’iyyar Democrat, su na shirye-shiryen zabubbukan tsaida dan takarar shugaban kasa guda biyu na jam’iyyarsu da suka rage a gobe talata.

A jiya lahadi, Uwargida Clinton ta samu gagarumar nasara a zaben fitar da gwani a yankin Puerto Rico, amma har yanzu Obama yana ci gaba da ba ta rata a yawan wakilan da ake bukata don zamowa dan takara na jam’iyyar.

Obama yana bukatar goyon bayan karin wakilai kimanin hamsin nan gaba domin ya samu wakilai dubu biyu da 118 da ake bukata don lashe wannan takara. Kwamitin yakin neman zaben Obama yana da kwarin guiwar cewa dan takarar nasa zai samu yawan kuri’un da ake bukata nan da karshen makon nan a bayan jihohin Dakota ta Kudu da Montana dake yammacin kasar nan sun gudanar da zabubbukan fitar da dan takararsu gobe talata, tare kuma da goyon bayan wasu daga cikin wakilai masu zaman kansu wadanda har yanzu ba su fitar ad gwani ba.

Wakilai masu zaman kansu dai shugabannin jam’iyya ne da wadanda aka zaba bisa wani mukami karkashin inuwar jam’iyyar wadanda suna da ikon zaben duk wanda suke so.

Wannan takara a tsakanin Uwargida Clinton da Obama tana ci gaba duk da cewa tuni jam’iyyar Republican ta san dan takararta. Wannan ya haddasa fargabar cewa kawunan ’yan Democrat na iya rarrabuwa. Wasu shugabannin jam’iyyar sun bukaci wakilai masu zaman kansu da su fito su bayyana goyon bayan dan takara guda a wannan makon don gujewa ci gaba da kai ruwa ranar da ake yi.

XS
SM
MD
LG