Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sa'udiyya Ta Ce Zata Kira Taro Don Tattauna Tashin Farashin Babu Gaira Babu Dalili Da Man Fetur Keyi


A yau litinin kasar Sa’udiyya ta ce zata kira taro a tsakanin kasashe masu arzikin mai da kasashen dake sayen man domin tattauna abinda jami’ai suka kira tashin farashi na babu gaira babu dalili da mai keyi.

Farashin gangar mai ya cilla sama zuwa dala 139 da wasu kwabbai ranar jumma’a, amma ya sauko kasa kadan tun daga lokacin.

Jami’ai a kasashe masu arzikin mai sun ce ba karancin man ne yake haddasa tashin farashin ba, ’yan kashe-mu-raba na kasuwannin mai ne da kuma tankiyar siyasa.

Shugaba George Bush na Amurka ya bayyana damuwa dangane da hauhawar farashin man da kuma tattalin arziki kafin ya tashi zuwa Turai.

XS
SM
MD
LG