Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya yayi Tur Da Cin Zarafin 'Yan Hamayya Da Ake Yi A Zimbabwe


Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, yayi tur da tashin hankali da kuma cin zarafin da ake yi wa 'yan hamayyar siyasa na kasar Zimbabwe, yana mai fadin cewa ba zai yiwu a gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa tsakani da Allah cikin wannan yanayi a ranar jumma'a ba.

Ba tare da wata hamayya ba, dukkan wakilai 15 na Kwamitin Sulhun sun yarda da wata sanarwar da aka rage kaifin lafazinta wadda ta yi tur da farmakin da ake kaiwa kan 'yan hamayyar siyasar gwamnati kafin zagaye na biyu na zaben da za a yi.

Wannan shi ne karon farko da Kwamitin Sulhun MDD ya dauki wani mataki a kan rikicin kasar Zimbabwe.

Tun da fari a litinin, babban sakataren MDD, Ban Ki-moon, yayi kira ga Zimbabwe da ta jinkirta zaben na ranar jumma'a, yana mai fadin cewa duk wata kuri'ar da za a jefa a cikin wannan yanayi ba zata samu halalci ba.

Madugun hamayya, Morgan Tsvangirai, wanda tun farko ya gudu ya nemi mafaka a ofishin jakadancin kasar Netherland dake Harare, ya janye daga zagaye na biyu na zaben da za a yi tsakaninsa da shugaba Robert Mugabe, yana mai fadin cewa an kashe magoya bayan jam'iyyar hamayya masu yawa, wasu kuma an ji musu raunuka.

Jakadan Zimbabwe a MDD, Boniface Chidyausiku, yayi watsi da rahotannin tashin hankali, ya kuma ce za a gudanar da zaben ranar jumma'a kamar yadda aka shirya.

Jiya litinin, 'yan sanda sun kai sumame a hedkwatar jam'iyyar MDC ta Mr. Tsvangirai a Harare. Wani kakakin jam'iyyar ya ce 'yan sanda sun kama mutane kimanin sittin, akasarinsu mata da yara kanana. 'Yan sanda suka ce mutane talatin da tara suka kama.

XS
SM
MD
LG