Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kasashe Masu Arzikin Masana'antu Zai Mayar Da Hankali Kan Sauyin Yanayi Da Wasu Batutuwan


Batutuwan sauyin yanayi, da tabarbarewar tattalin arzikin duniya, da hauhawar farashin mai da na abinci sune muhimmai a cikin ajandar tattaunawar da ake yi yau talata a taron kolin manyan kasashe takwas mafiya arzikin masana’antu na duniya a kasar Japan.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta fadawa ’yan jarida cewa ta "gamsu sosai" da tattaunawar da ake yi a game da matsayin kungiyarsu kan sauyin yanayi, a bayan da ta tattauna ido da ido da shugaba George Bush na Amurka. Masu kula da lamarin sun ce Mr. Bush yana shan matsin lamba a kan ya goyi bayan kayyade takamammen adadin iskar guba mai kara dumama duniya da ake fitarwa, abinda ya ce ba zai yi amfani ba idan har ba a shigar da kasashe masu bunkasar tattalin arziki kamar Indiya da kasar Sin a ciki ba.

Nan gaba a yau ake sa ran shugabannin zasu bayar da sanarwa kan yadda za a takali sauyin yanayi da wasu batutuwan.

Jiya litinin, shugabannin Afirka sun roki kasashen takwas masu arzikin masana’antu da su cika alkawarin da suka yi na kara yawan agajin da suke bai ma Afirka zuwa dala miliyan dubu 25 kowace shekara nan da 2010. Babban sakataren MDD, Ban Ki-moon ya goyi bayan shugabannin na Afirka yana mai fadin cewa matsalolin abinci da sauyin yanayi da kuma raya kasa duk suna da alaka da juna.

XS
SM
MD
LG