Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Radovan Karadzic


Dakarun tsaron Serbia sun kama tsohon madugun 'yan kabilar Sabiyawan Bosniya, Radovan Karadzic, daya daga cikin mutanen da aka jima ana nema ruwa a jallo a duniya, ana kuma tuhumarsa da aikata laifuffukan yaki.

Ofishin shugaba Boris Tadic na Serbia, shi ya ba da sanarwar kama Karadzic litinin, amma bai yi karin bayani ba. A yanzu, Karadzic yana hannun Kotun Bin Kadin Laifuffukan Yaki ta Serbia a birnin Belgrade, yana jiran yiwuwar mika shi ga Kotun Bin Kadin Laifuffukan Yaki ta Majalisar Dinkin Duniya dake birnin Hague a kasar Netherlands.

Kotun ta Hague ta tuhumi Karadzic da aikata laifuffukan kisan kare-dangi, cin zarafin bil Adama da wasu munanan laifuffukan da dama.

Babban mai gabatar da kararraki a kotun ta Hague, Serge Brammertz, ya taya hukumomin kasar Serbia murnar damke Karadzic. Ya bayyana kama mutumin a zaman wata babbar tazara, kuma muhimmiyar rana ga mutanen da suka tagayyara a sanadin Karadzic. Brammertz ya ce kama Karadzic da aka yi ya nuna cewa babu wani mahalukin da zai iya tsere ma doka.

Ita ma Kungiyar Tarayyar Turai ta yaba da kama tsohon madugun na Sabiyawan Bosniya. Tarayyar ta maida batun kama mutanen da ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki wani sharadi mai muhimmanci na shigar da kasar Serbia cikin wannan kungiya.

Karadzic ya shafe shekaru fiye da goma sha biyu yana buya. A matsayinsa na shugaban 'yan kabilar Sabiyawan Bosniya lokacin yakin shekarun 1990, ana zarginsa da laifin bayar da umurnin hallaka dubban mutanen da ba 'yan kabilar Sabiyawa ba, ciki har da wasu mazaje Musulmi su fiye da dubu takwas, yara da manya, wadanda aka tattara su aka je aka kashe su a garin Srebrenica a shekarar 1995.

Karadzic yana cikin shugabanni hudu na yankin Balkan a lokacin yaki wadanda kotun bin kadin laifuffukan yaki take nemansu ruwa a jallo. har yanzu ana farautar kwamandan sojojin Sabiyawan Bosniya, Ratko Mladic da tsohon madugun 'yan kabilar Sabiyawan Croatia, Goran Hadzic.

A watan da ya shige 'yan sandan Serbia suka kama tsohon kwamandan 'yan sanda na kabilar Sabiyawan Bosniya, Stojan Zupljanin.

XS
SM
MD
LG