Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda A Indiya Sun Warware Bama-Bamai Guda Biyu...


Hukumomin Indiya sun warware wasu bama-bamai guda biyu a birnin Ahmedabad, kwana guda a bayan da aka kashe mutane akalla 45 a hare-haren bam a wannan birni.

An gano wadannan bama-bamai jiya lahadi, a lokacin da jami'an tsaro suka bazu a babban birnin harkokin kasuwanci na Jihar Gujarat a yammacin kasar Indiya. A ranar asabar, an kai jerin hare-haren bam biyu a Ahmedabad, inda aka auna wata kasuwar dake cike da mutane da kuma wani asibiti. Mutane 160 suka ji rauni.

'Yan sandan Indiya sun ce an tsare mutane kimanin 30 domin yi musu tambayoyi.

Haka kuma a jiya lahadin, 'yan sanda a Jihar Gujarat sun gano wata mota dauke da nakiyoyi a birnin Surat dake kudu da birnin Ahmedabad. Haka kuma, 'yan sandan Indiya sun kai sumame a kan wani gida a birnin Mumbai. Ana zaton daga wannan gida ne wata wasikar Email dake daukar alhakin kai hare-haren ta fito.

Wata kungiyar da ba a san da ita sosai ba da ta kira kanta Mujahidin ta Indiya, ta dauki alhakin hare-haren a cikin wata wasikar Email da aka aika 'yan mintoci kadan kafin bama-baman su fara tashi.

Ana sa ran firayim ministan Indiya, Manmohan Singh, zai yi tattaki zuwa Ahmedabad yau litinin domin ziyartar wadanda suka ji rauni.

XS
SM
MD
LG