Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Litinin Jacob Zuma Zai Bayyana Gaban Kotu A Afirka Ta Kudu


A yau litinin shugaban jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, zai bayyana gaban kotu inda zai yi kokarin ganin an fatattaki tuhumar zarmiya da cin hancin da ake yi masa wadda kuma tana iya hana shi zama shugaban kasar a shekara mai zuwa.

A watan Disamba aka tuhumi Zuma da laifin hada baki don zamba, da zarmiya, da batar da sawun kudin haramun da kuma zamba cikin aminci. Ana sa ran zai gabatar da takarda a gaban babbar kotu inda zai kalubalanci shawarar da gwamnati ta yanke ta gurfanar da shi gaban shari'a.

Wannan shine karo na biyu da aka yi kokarin gurfanar ad Zuma gaban kotu bisa zargin zarmiya. A shekarar 2006, wani alkali ya kori karar da aka shigar ta Zuma.

Ana sa ran cewa magoya bayan Zuma, wadanda suka ce wata makarkashiyar siyasa ce ta sa ake tuhumarsa, za su bayyana a kotun da yawan gaske. Wata mai magana da yawun 'yan sanda ta ce an tura karin 'yan sanda zuwa garin Pietermaritzburg, inda za a yi wannan shari'a. Ana kyautata zaton yadda shari'ar zata kaya ita ce za ta tantance ko Zuma zai gaji Thabo Mbeki a matsayin shugaban Afirka ta Kudu a 2009

XS
SM
MD
LG