Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar Democrat ta Amurka, a makon gobe, zatayi taron ta na kasa a Denver,Colorado.


Jam'iyyar Democrat ta Amurka, a makon gobe, zatayi taron ta na kasa a Denver,Colorado. Za a fara taron, daga 25 zuwa 28, na watan Agusta, 2008.

A lokacin taron ne Jam'iyyar Democrat ta Kasa,zata tsaida Senata Barack Obama,takarar shugabancin Amurka.

Fitattun mutane da dama ne zasu yi jawabai a taron na kwana hudu. A jerin farko na masu yin jawabai, har da babbar abokiyar hamayyar sa, a zazzafar yakin share fagen tsaida dan takara na Jam'iyyar,Senata Hillary Clinton,da mai gidanta,tsohon shugaban kasa Bill Clinton.

Haka kuma a yini na farkon, Michelle Obama,uwargidan senata Obama,kakakin Majalisa Nancy Pelosi,da kuma tsohon shugaban kasa Jimmy Carter,suna cikin masu gabatar da jawabai. Taken jawaban wannan yini, shine:Kasa Daya,Al'uma Daya.

XS
SM
MD
LG