Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau litinin dinnan abude babban taron Jam’iyyar Democrat a Denver, jihar Colorado


Yau litinin dinnan abude babban taron Jam'iyyar Democrat a Denver, jihar Colorado, inda ake sa ran a karon farko a tarihi, za a tsaida bakar fata dan asalin Afirka a matsayin dan takarar shugabancin kasa, a nan Amurka.

Za a kwashe kana hudu ana wannan taro, wanda zai hada da tarukan gangami, da jawabai daga hanshakan 'yan jam'iyya, daga karshe kuma a karkare da jawabin Sanata Barack Obama, inda zai amince da zabin da jam'iyyar tayi masa na yayi mata takara.

Ita kuma Jam'iyyar Republican, a mako mai zuwa zata yi nata taron. Wadannan taruka dai sune ke bude yakin neman zaben Shugaban kasa da za a guidanar a watan Nuwamba mai zuwa.

McCain dai bai fita bainar jama'a ba a jiya Lahadi, amma dai kwamitin yakin neman zabensa ya fitar da wata sanarwa a talbijin, inda yake sukan lamirin Barack Obama.

A wani labarin kuma, Shugabannin Jam'iyyar Democrat sun dawowa da wakilan jihohin Michigan da Florida, damar su ta kada kuri'a, wadda aka janye saboda a hukunta su, sakamakon kunnen kashin da suka nuna, na gudanar da zaben fitar da gwani kafin ranar da aka tsayar masu.

XS
SM
MD
LG