Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton ta kirayi illahirin ‘Yan ‘Jam’iyyar Democrat, su marawa Obama


Uwargida Hillary Clinton ta kirayi illahirin ‘Yan ‘Jam’iyyar Democrat, su marawa Obama baya wajen ganin an zabe shi shuagaban Amurka. Tana mai cewa,Jam’iyyar bata da “zarafin yin soko soko koda na dakiki ko kuri’a daya” bisa wannan yunkuri.

Tayi magana ne jiya da daren Talata, a taron Jamiyyar Democrat na kasa a Denver,Jihar Colorado,inda Obama zai karbi tutar Jam’iyyar na zame mata dan takarar shugabancin Amurka gobe Alhamis idan Allah ya kaimu.

XS
SM
MD
LG