Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwa na pantsama ya tsallaka  manyan katangu da aka gina a New Orleans


Ruwa na pantsama ya tsallaka manyan katangu da aka gina a New Orleans,duk da haka shugabanni sun hakikance ba zasu rushe ba,duk da farmakin da mummunar guguwar tekun mai karfin gaske (Gustav) take kawowa.

Guguwar bata dira kai tsaye kan birnin New Orleans yau litinin,ta sauka doron kasa da nisan kilomita 110 kudu maso yammacin New Orleans. Guguwar Gustav ta isa doron kasa a rukuni na biyu da iska dake gudun kilomita 175 cikin ko wace sa'a daya.

Ana sa ran zata fatattaki birnin na sa'o'I masu yawa. Hukumomi sunce kamar kashi 95 cikin dari na mazauna yankin da iskar takewa barazana sun kwashe na su ye nasu sun tsere,saboda tuna irin barnar da wata guguwar Katrina ta yi a wannan yankin shekaru uku da suka wuce. Katrina ta rusa ganuwar tare ruwa, da aka gina,sakamakon haka kashi 80 cikin dari na birnin ya cike daruwa.

XS
SM
MD
LG