Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Laraba  taron Jam’iyyar Republican zata ayyana tsaida dan takarar shugaban kasa John McCain,da matai makiyar sa Sarah Palin.


A daren yau Laraba ce wakilai dake halartar babban taron Jam'iyyar Republican zasu ayyana tsaida mai yiwa Jam'iyyar takarar shugaban kasa John McCain,da matai makiyar sa Sarah Palin.

Ana sa ran Palin zata yi na'am da tsaidata 'yar takara a wani jawabi da ake dokin sa a muhimmin lokaci da Amurkawa ke maida hankali ga talabijin a daren na yau,domin gabatar da ita garesu. McCain da mai dafa masa baya sun sami dumbin goyon baya daga fitattun magoya baya,ciki har da shugaba George Bush, a taron Jam'iyyar na jiya da dare.

Da yake magana ta taurawurar dan'adama daga Fadar White House,Mr. Bush yace Mccain ya san hanyoyin kare Amurka daga harin masu kisa ta'addanci.Ya kuma yaba masa saboda goyon bayan da McCain ya bayar ga shirin tura karin sojoji Iraqi. Ga rahoton da Dan Robinson ya aiko mana.

XS
SM
MD
LG