Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Isra'ila Sun Bada Shawarar A Tuhumi Firayim Minista Ehud Olmert Da Laifuffuka Na Zarmiya


'Yan sandan bani Isra'ila sun bayyana cewa su na son a tuhumi firayim minista Ehud Olmert a gaban kotu dangane da wani abin fallasa na zarmiya da cin hanci.

Wakilin Muryar Amurka a birnin Qudus, Robert Berger, ya ambaci ’yan sandan su na fadin cewa akwai wadatacciyar shaidar tuhumar firayim minista Olmert da laifuffuka biyu na zarmiya. Suka ce Mr. Olmert ya karya doka ta hanyar karbar takardun ambulon da aka cika da tsabar kudi daga wani bayahude dan kasuwa dan Amurka, da kuma neman da a biya shi sau biyu ko sau uku daga baitulmali na tafiye tafiyen da yayi a waje.

An yi zargin cewa wannan ya faru cikin shekaru 15 da Mr. Olmert yayi yana minista kuma magajin garin birnin Qudus.

Mai fashin bakin harkokin shari’a na Isra’ila, Dan Eisenberg, ya ce atoni janar na Isra’ila ne yake da ikon yanke shawara kan tuhuma, kuma yin hakan yana iya daukar tsawon lokaci.
Eisenberg ya ce, "akwai masu hasashen cewa zai yanke shawara a cikin makonni biyu, amma a gaskiya koda yayi hakan ma, shawarar zata zamo ta wucin gadi ne a saboda tilas ya bada Mr. Olmert damar zuwa a saurare shi kan batun, kuma yin hakan zai dauki watanni. A saboda haka har yanzu za a dauki lokaci mai tsawo kafin a samu shawara ta karshe."

Mr. Olmert ya musanta cewa ya aikata wani laifi, amma a saboda matsin lambar jama’a da kuma jam’iyyarsa, ya shirya yin murabus nan gaba cikin wannan watan. Amma a karkashin tsari mai sarkakiya na gudanar da gwamnati a Isra’ila, yana iya ci gaba da zama kan wannan kujera na karin wata da watanni a matsayin firayim ministan riko.

Mr. Olmert ya ce zai ci gaba da kokarin ganin an samu ci gaba a tattaunawar neman zaman lafiya da Falasdinawa da kuma kasar Syria har ya zuwa ranarsa ta karshe kan wannan kujera.

XS
SM
MD
LG