Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Nijeriya Su Na Gwabza Kazamin Fada Da 'Yan Tsageran Niger Delta


Babbar kungiyar ’yan tsagera a yankin Niger Delta ta Nijeriya, ta ayyana yaki gadan-gadan a kan cibiyoyin mai, a bayan da aka shafe kwanaki biyu ana gwabza kazamin fada a tsakaninta da sojojin gwamnatin kasar.

Wakilin Muryar Amurka, Gilbert Da Costa, ya ce kungiyar ta MEND ta lashi takobin dauko fansar farmakin da sojoji suka kai a kan sansanoninta ranar asabar.

Kungiyar ta MEND mai ikirarin kare muradun yankin Niger Delta, ta gargadi kamfanonin mai da su janye ma’aikatansu a cikin kwana guda daga ranar lahadi, ko kuma su fuskanci abinda ta kira guguwar hare-haren ramuwar gayya.

Masu fashin baki sun ce an kara zafafa yawa da kuma munin hare-hare a yankin Niger Delta a saboda al’amura suna kubucewa daga hannun dakarun gwamnati. Shugaban Nijeriya, Umaru Musa ’Yar’aduwa, yana shan matsin lamba a kan ya murkushe wannan fitinar.

Farmakin da sojojin Nijeriya suka kai a karshen mako, watakila alama ce ta sabuwar manufar babu sani babu sabon da gwamnati ta runguma kan tsageranci a yankin Niger Delta. Amma ’yan tsageran sun ce ba su jin tsoron gwabzawa da rundunar sojoji. Wani kwamandan ’yan tsagera, Tom Polo, yayi magana da Muryar Amurka, inda yake cewa, "...Mu na shirin kara yawan hare-haren da muke kaiwa kafin ranar bukin kewayowar ’yancin kan Nijeriya, watau 1 ga watan Oktoba. Mu na da dakaru da makaman da zasu iya fuskantar sojojin gwamnati."

Tashin hankalin da aka shafe kusan shekaru 20 ana yi a yankin Niger Delta ya rikide cikin ’yan shekarun nan ya koma tawaye na neman mallakawa mutanen yankin arzikin man fetur na yankinsu. ’Yan tsageran suka ce yankin Niger Delta ba ya samun kason da ya kamata daga cikin dimbin arzikin da yake samarwa ga kasar. Yunkurin da gwamnati ta yi na tattaunawa da ’yan tsageran ya wargaje a watan Agusta.

An sace ’yan kasashen waje su kusan 300 a yankin Niger Delta tun farkon shekarar 2006. Kusan dukkansu kuwa an sako su lafiya a bayan da aka biya kudin diyya. Har yanzu ana rike da wasu ma’aikatan mai su 27 da aka sace a makon da ya shige.

XS
SM
MD
LG