Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alan Greenspan,Tsohon Gwamnan Babban Bankin Amurka Ya bada Shaida Gaban Majalisar Dokokin Amurka kan Rikicin Kudi Da Amurka Take Fama Dashi


Tsohon shugaban Babban Bankin Amurka, Alan Greenspan ya bayyana matsalar da yanzu ake fuskanta a tsarin cinikayya da tattalin arziki salon na jari hujja da sunan girgizar tekun tsunami da bata faruwa sai a sau ɗaya cikin ƙarni guda.

A jawabin bada shaidar da yayi yau Alhamis a gaban kwamatin majalisar dokokin Amurka, an nemi da ya bada shawarar hanyar fita daga wannan ƙangi, ya kuma gano musabbabin taɓarɓarewar tsarin tattalin arzikin domin a ɗauki matakan hana irin hakan sake afkuwa.

Duk da haka Mr.Greenspan yayi kashedin ƙarfafa takurawa tsarin cinikayyar kamfanoni, abinda ya riƙa watsi da yi a tsahon shekaru goma sha takwaas da yayi yana jagorancin Baitul malin Amurka. Amma Greenspan ya amince da ƙarfafa aiki da matakan takurawar koda yake hakan zai sa kamfanonin su riƙa korar ma’aikata masu yawa, a kuma kai ga samun maras aikin yi masu yawa a Amurka.

XS
SM
MD
LG