Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin Jama'a Game Da Zaben Obama


Ojo na titin Bugaje (titinbougajeojo@yahoo.fr) BP : 486 Zinder a Jamhuriyar Nijar, ya rubuto yana cewa, "...sashen hausa na muryar amurka ku gayama shuwagabannin siyasa na kasarmu Niger, Zaben kasar Amurka ya kamata ya zame musu ishara, saboda sunga yinda dan adawa zai fadi a takarar neman kuri'a ta zabe, kuma ya amince da lalle ya fadi, sannan ya kirayi magoya bayenshi da su mara ma wanda yaci domin a tafi tare dan ama kasa aiki, a gaskia wannan abu sai a Amurka. Allah yasa shuwagabanninmu wannan ishara zata zamo musu karatu a kayunansu, amin."

IBRAHIM JATAU MAI NAMA BISIJE MALUMFASHI, tare da YUSUF MAIKANO LUNGUN ALHAZAWA MALUMFASHI, sun rubuto su na cewa, "Barak Obama yau an wayi gari ALLAH yasa ka zama shugaban kasar Amurka, saura ka cika alkawuran duk da ka dauka, ka kuma yi kokarin dawo da martabar AMURKA A IDANUN DUNIYA."

"Hakika Amirkawa tabbas kunzama zakarar gwajin dafin duniya, ga shi kunyi zabenku lafiya cike da adalci, da sanin yakamata, to, Obama sai ka rike kowa hannu biyu biyu, sannan kada kamanta da irin goyon bayan da 'yan uwanka al'umar Afirka suka baka. To, yaya babbar kwabo wato Najeriya kinga yanda ake tafiyar da zabe cikin adalci, ba 'yan banga. ba fisge akwatun zabe, babu aiki da 'yan sanda dan su musguna ma masu kada kuri'a, to, yaya babbar kwabo Najeriya sai kigyara tsarin zabenki indai kina son kici gaba da hura hanci a kasashen Afirika." Daga Sani World 7 Kusfa Zaria.(Saniworld7kusfazaria@yahoo.com)

SHUAIBU MUHAMMED RIJIYAR MAIKABI(RKB20042001@YAHOO.COM)ya rubuto ta sa takardar yana fadin cewa, "Ra'ayina shine In nuna farin cikina kan yadda "yan kasar Amuruka suka debewa kansu takaici suka tsaya suka nuna su na da "yanci sannan inyi kira ga sabon Shugaban kasar ta Amuruka wato Barack Obama da ya cika Alkawalinda yadauka yatsaya tsayin daka don maido wa kasar Amuruka martabarta."

Muhammed Usman Dandattijo Bayan NEPA, Malumfashi, Jihar Katsina, ya ce, "Assalamu alaikum ina taya Barack Obama da sauran al'umar Afrika dama duniya baki daya murnar samun nasarar cin zaben dan'uwanmu Barack Obama. Allah Ya yi masa jagora da fatan zai ba marada kunya."
XS
SM
MD
LG