Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miriam Makeba Ta Rasu


Shahararriyar mawakiya, kuma 'yar rajin 'yancin siyasa ta Afirka ta Kudu, Miriam Makeba, ta rasu tana da shekaru 76 da haihuwa.

Yau litinin Miriam Makeba ta rasu a kasar Italiya a bayan da ta gabatar da wani wasa na tallafawa wani marubuci mai suna Roberto Saviano, wanda 'yan Mafia suka yi barazanar kashewa.

Makeba ta fara rashin lafiya a bayan gudanar da wasan, sai aka dauke ta zuwa asibiti a Castel Volturno. Kamfanin dillancin labaran ANSA na Italiya ya ce da alamun ciwon bugun zuciya ne ya kamata.

Masoyan Miriam Makeba sun lakaba mata sunan "Mama Africa". Muryarta da wakokinta sun zamo tamkar tambarin yaki da wariyar launin fata. A shekarar 1959, gwamnatin wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu ta tilasta mata yin gudun hijira, kuma ba a kyale ta ta koma kasar ba sai a shekarar 1990, a bayan da aka sako Nelson Mandela daga gidan kurkuku.

A shekarar 1965, Makeba ta sami lambar yabon waka ta Grammy tare da wani mawaki mai suna Harry Belafonte a saboda wani faifan hadin guiwa da suka yi.

XS
SM
MD
LG