Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Mika Kuka Ga Hukumomin Nijeriya Kan Kagen Da Ta Ce An Yi Ma 'Yan Kasarta A Jos


Nijar ta mika takardar kuka ga hukumomin makwabciyarta Nijeriya dangane da kagen da ta ce an yi mata kan ta kyale 'yan kasarta sojojin haya sun shiga cikin mummunan fadan addini.

A ranar talata ce gwamnatin Jihar Filato ta ce ta kama wasu 'yan Nijar su 16 a bayan da aka kashe daruruwan mutane a rikicin addini a garin Jos. Hukumomin na Jihar Filato sun yi zargin cewa wadannan 'yan Nijar sun yi tattaki zuwa Jos din ne da nufin gwabza fadan addini.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta fada yau alhamis cewar ta mika takardar kuka da babbar murya ga Nijeriya, inda balo-balo ta karyata wannan zargin da ta ce ba ya da wata madafa. Ma'aikatar ta fada cikin wata sanarwa cewa mutanen da aka kama, mutane ne da suka yi shekara da shekaru su na zaune a Jos su na yin sana'a a can.

Sanarwar ta ce an tura jakadan Nijar a Nijeriya, Isa Ibrahim, zuwa Jos domin ya ganewa idanunsa yadda al'amura suke a can.

XS
SM
MD
LG