Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Annobar Kwalara Tana Kara Yin Muni A Zimbabwe


Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta ce anobar kwalara tana ci gaba da kara yin muni a kasar Zimbabwe, inda a yanzu yawan mutanen da suka mutu daga wannan cuta ya tashi zuwa fiye da dubu daya da dari daya.

Sabon alkalamin da aka bayyana yau alhamis ya nuna karuwar mutuwar mutane 133 a cikin kwanaki biyu kacal.

Ofishin Kula da Ayyukan Jinkai na MDD, ya ce daga watan Agusta zuwa yanzu, , mutane fiye da dubu ashirin da dari biyar ne suka kamu da cutar. A yau alhamis, Ofishin ya ba da rahoton barkewar sabuwar annoba ta kwalara a Chegutu, wanda ke yamma da Harare, babban birnin kasar, inda ofishin ya ce an samu rahoton tabbacin mutane 378 dauke da cutar da kuma mutuwar wasu mutanen su 121.

MDD ta ce rashin ruwan sha mai kyau da kuma kazanta su na ci gaba da zama matsala babba, yayin da akasarin ma'aikatan kiwon lafiya na Zimbabwe suke yajin aiki.

Kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa nan da farkon shekara mai zuwa za a fuskanci karewar ruwan da ake durawa marasa lafiya ta allura. Irin wannan ruwan magani da ake durawa ta jiki ne ake amfani da shi wajen jinyar masu fama da cutar kwalara.

XS
SM
MD
LG