Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Benedict Yayi Kiran Da A Samu Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya Da Afirka


Paparoma Benedict yayi kiran da a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da Afirka a cikin sakonsa na Kirsimeti a fadar Vatican.

A lokacin da yake jawabi ga dubban mutane yau alhamis a majami'ar Saint Peter's Basilica dake birnin Rum, Paparoman yayi kiran da "hasken Bethlehem" ya yadu a duk Kasa Mai Tsarki, inda yace ana cikin mummunan hali a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Har ila yau Paparoman yayi jimamin halayyan da ake ciki a Zimbabwe, da Kwango-ta-Kinshasa da Darfur da kuma Somaliya.

A Bethlehem, inda aka haifi Yesu Kiristi, Babban Fada na Cocin Latin, Fouad Twal, shi ma yayi addu'ar samun zaman lafiya.

Twal, wanda shi ne shugaban Kiristoci masu bin darikar Katolika a Kasa Mai Tsarki, ya ce yaki ba ya haifar da zaman lafiya, gidajen kurkuku ba su tabbatar da kwanciyar hankali, haka kuma katanga ba ta tabbatar da tsaro komai girmanta.

Da yawa daga cikin Kiristocin da suka taru da tsakar dare domin sauraron Babban Fada Twal sai da suka bi ta cikin wata katangar kankare da ta raba Bethlehem da Qudus.

XS
SM
MD
LG