Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Zabe A Ghana Sun Ce Ba Za A Bayyana Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Ba...


Jami'an zabe a Ghana sun ce ba zasu bayyana wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi ranar lahadi ba har sai bayan an gudanar da zabe a wata mazaba guda da ta rage.

Jami'ai suka ce za a gudanar da zabe ranar Jumma'a a mazabar Tain inda tun farko aka samu karancin kuri'u.

Sakamakon farko ya nuna dan takarar jam'iyyar hamayya ta NDC, John Atta-Mills, yana gaban dan takarar jam'iyyar NPP mai mulkin kasar, Nana Akufo-Addo, da 'yar rata kadan.

Atta-Mills yana da kashi hamsin da digo daya cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da Akufo-Addo yake da kashi 49 da kusan digo 9 cikin 100.

Wanda ya lashe zaben zai maye gurbin shugaba John kuffour, wanda zai kammala wa'adinsa biyu na shekaru 8 a kan mulki.

An girka sojoji da 'yan sanda a hedkwatar hukumar zabe a Accra, babban birnin kasar, inda daruruwan magoya bayan jam'iyyar hamayya suka yi cincirindo. Dukkan jam'iyyun biyu sun zargi juna da laifin kuntatawa abokan hamayya da shirya murdiya.

XS
SM
MD
LG