Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Litinin Kotun Daukaka Kara Ta Afirka Ta Kudu Zata Yanke Hukumci Kan Shari'ar Jacob Zuma


Litinin din nan wata kotun Afirka ta Kudu take shirin yanke hukumci dangane da wata karar da ta shafi zargin zarmiya da cin hancin da ake yi ma Jacob Zuma, mutumin da ake zaton zai tsaya takarar shugaban kasa.

Masu gabatar da kararraki sun roki Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ta kawar da hukumcin da wata karamar kotu ta yanke inda ta watsar da tuhumar da ake yi ma Zuma, shugaban jam'iyyar ANC mai mulkin kasar. A watan Satumba karamar kotun ta yanke wannan hukumci, abinda ya share ma Zuma fagen tsayawa takarar shugaban kasa.

Shugabannin ANC sun ce ko da an ci gaba aka tuhumi Zuma da wadannan laifuffuka, shi ne zai tsaya ma jam'iyyarsu takarar shugaban kasa.

Masu gabatar da kararraki suka ce Zuma ya karbi cin hanci a hannun wani kamfanin da ya samu aikin kwangila mai tsoka na sayo makamai. Zuma ya musanta aikata wani laifi, yana mai fadin cewa 'yan uba na siyasa ne kawai suke makarkashiyar ganin bayansa.

XS
SM
MD
LG