Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebola


Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce annobar cutar da ta bulla a Kwango-ta-Kinshasa ba ta yadu zuwa kasar Angola, makwabciyarta ba.

Darektan yanki na hukumar WHO a Afirka, Luis Gomes Sambo, ya fadawa ‘yan jarida a birnin Luanda cewar babu wani dalili na tada hankali, kuma babu wata shaida da aka gani cewar kwayar cutar Ebola mai saurin yin kisa ta tsallaka bakin iyaka ta shiga Angola.

Mr. Sambo yayi magana da ‘yan jarida ne a bayan da ya gana da shugaba Jose Eduardo Dos Santos na Angola, inda yayi masa bayanin barkewar annobar cutar Ebola da ta kashe mutane akalla 14 ya zuwa yanzu a yankin kudu maso yammacin Kwango.

Akalla larduna biyu na kasar Angola sun rufe bakin iyakokinsu da kasar Kwango-ta-Kinshasa domin kawar da yiwuwar yaduwar wannan cuta daga makwabciyar ta su.

Cutar zazzabin Ebola mai haddasa yoyon jini daga sassan jikin bil Adama, tana daya daga cikin cututtukan da suka fi yin kisa a duniya, inda take kashe mutane hamsin zuwa mutane casa’in daga cikin mutane 100 da suka kamu da ita.

Ana daukar wannan cuta daga jini ko kuma ruwan jikin mai dauke da cutar, kuma ta kan haddasa jini yayi ta zuba ba tsayawa daga idanu, kunnuwa, baki da wasu sassan jikin da

XS
SM
MD
LG