Faransa ta ce sojoji biyu sun mutu, wasu shida kuma sun bace a lokacin da wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojoji ya fada cikin teku a daura da gabar kasar Gabon. An ceto wasu sojojin su biyu.
Wannan jirgin helkwafta samfurin Cougar na sufuri, yana dauke da sojoji 10 a lokacin da ya fada cikin teku jim kadan a bayan tashinsa daga wani jirgin ruwan yaki na Faransa asabar din nan. Sojojin na Faransa su na cikin masu gudanar da atusayen soja na hadin guiwa a tsakanin Faransa da Gabon ne.
Masu aikin ceto su na neman wadanda suka kubuta da rai lahadi a dab da gabar Nyonie, wani gari dake tsakanin Libreville, babban birnin kasar ta Gabon, da garin Port Gentil mai tashar jiragen ruwa.
Shugaba Nicolas Sarkozy ya bada umurnin da a yi amfani da duk wani abinda kasar Faransa ke da shi domin samo sojojin da suka bata. Haka kuma ya tura ministan tsaron Faransa, Herve Morin zuwa yankin.
Ba a san dalilin da ya sa wannan jirgi ya fadi ba.