Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Mako Mai Zuwa Jacob Zuma Zai San Ranar Fara Shari'arsa


A mako mai zuwa ne shugaban jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu zai ji ko yaushe ne za a fara shari'arsa bisa zargin cin hanci da rashawa. Jaridar Sunday Times ta bayar da rahoton cewa Jacob Zuma zai bayyana a gaban Babbar Kotun Pitermaritzburg ranar 4 ga watan Fabrairu inda za a tsaida ranar fara yi masa shari'ar.

Ana sa ran cewa Zuma, wanda shi ne shugaban jam'iyyar ANC, zai zamo dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zabe mai zuwa.

Masu gabatar da kararraki sun sake tuhumar Zuma da laifin cin hanci da rashawa a makon jiya, a bayan da kotun daukaka kara ta ce wata karamar kotu ta yi kura-kurai masu yawa a lokacin da ta watsar da tuhumar da ake yi ma Zuma. A watan satumba karamar kotun ta yi watsi da tuhumar da ake yi ma Zuma, tana mai hasashen cewa tsohon shugaba Thabo Mbeki, abokin hamayyar Zuma a cikin jam'iyyar ANC, ya nemi yin katsalanda a shari'ar.

XS
SM
MD
LG