Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Madugun Sojojin Sa Kai Na Kwango-Ta-Kinshasa Ya Bayyana Gaban Kotun Duniya


Wani tsohon madugun sojojin sa kai na Kwango-ta-Kinshasa ya zamo mutumin farko da aka gurfanar a gaban Babbar Kotun Bin Kadin Manyan Laifuffuka Ta Duniya (International Criminal Court ko ICC a takaice), bisa zargin aikata laifuffukan yaki.

Ana tuhumar Thomas Lubanga da laifin tilastawa yara kanana shiga aikin soja da yin amfani da su a matsayin sojojinsa a fadan da aka gwabza a gabashin kasar Kwango-ta-Kinshasa a 2002 da 2003. Lubanga ya musanta wannan zargi.

Masu gabatar da kararraki na kotun su na binciken wadanda ake zargi da aikata laifuffukan yaki a kasashen Afirka 4, amma Lubanga shi ne mutum na farko da ya gurfana gaban kotun.

An kafa wannan kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya, mai hedkwata a kasar Netherlands, a shekarar 2002 domin yin shari’ar laifuffuka mafiya muni na yaki da na cin zarafin bil Adama da kuma na kisan kare dangi. An kafa kotun bisa yarjejeniyar da kasashe 108 suka kulla cikinsu har da Kwango ta Kinshasa.

XS
SM
MD
LG