Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sashen Hausa Na Muryar Amurka Yana Bukukuwan Cika Shekaru 30


A cikin wannan makon ne Sashen hausa na Muryar Amurka yake kaddamar da bukukuwan cikar shekaru 30 da kafuwa. Sashen ya fara gabatar da shirye-shiryen Hausa a ranar 21 ga watan Janairun 1979, amma a saboda bukuwan rantsar da sabon shugaban Amurka da aka yi a makon, sai aka dage zuwa wannan makon da muke ciki.

A cikin wata sanarwar da ya bayar a nan Washington, shugaban Sashen Hausa, Sunday Dare, ya ce uwargidan shugaban Nijeriya, Hajiya Turai 'Yar'aduwa, ita ce zata jagoranci babban bukin da za a gudanar a ranar alhamis, 29 ga watan Janairu.

Wadanda zasu tallafa mata wajen jagorancin wannan bukin, sun hada har da gwamnonin jihohin Sakkwato, Kebbi, Yobe da kuma Filato. Tuni har wasu daga cikin bakin da za su halarci wannan buki sun iso nan birnin Washington.

A bangaren shirye-shirye kuma, tun daga shirin safiyar talata za a fara gabatar da wasu shirye-shirye masu nasaba da tarihin kafa wannan Sashe, da kuma yadda ya taso har ya zuwa wannan matsayin da ake daukarsa a zaman daya daga cikin mafiya tasiri a duniya.

Za a bada masu sauraro damar su bayyana ra'ayoyinsu a kan Sashen Hausa na Muryar Amurka a cikin shirye-shirye na musamman da za a yi ta gabatarwa a duk tsawon wannan makon.

XS
SM
MD
LG